Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi tir da hare haren da sojojin HKI suka kai kan karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Damascus na kasar Siriya. Ya kuma ja kunnen HKI kan cewa idan bata yi hankali ba, yakin da take yi a Gaza yana iya yahudawa a yankin ya kuma jawo musibu da dama ga fararen hula.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin babban sakataren yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma yi kira ga kasashen yankin Asiya ta kudu su mutunta dokokin kasa da kasa wadanda suka shafi diblomasiya. Da kuma mutuncin ko wace kasa a duniya.
Ya ce a halin da ake ciki a yankin kuskure kadan yana iya jefa dukkan yankin Asiya ta kudu cikin yaki da kuma asarorin rayuwa da dukiyoyi masu yawa.
A ranar litinin da ta gabata ce jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Damascus babban birnin kasar Siriya inda Janar Zahidi da Janar rahimi na dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC da wasu mutane 5 tare da su suka yi shahada.