Ayyukan Tallafawa Falastinawa A Rafah Na Fuskantar Babban Cikas Saboda Hare-Haren Isra’ila

Hukumar Kula da ayyukan tallafawa Falastinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNRWA ta ce an dakatar da rabon abinci a kudacin Rafah saboda rashin tsaro da

Hukumar Kula da ayyukan tallafawa Falastinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNRWA ta ce an dakatar da rabon abinci a kudacin Rafah saboda rashin tsaro da kuma ƙarancin abincin.

UNRWA ɗin ta bayyana haka a wata sanarwar da ta fitar a shafin X inda ta ce cikin cibiyoyinta 24, guda shida ne kaɗai ke aiki kuma su ma ba su samu wasu kayayyakin kiwon lafiya ba fiye da kwana 10 sakamakon rufe iyakar Rafah da Karem Shalom zuwa cikin Gaza.

Hare-haren da Isra’ila ta kai lokaci guda a yankunan kudanci da arewacin Gaza a wannan watan ya haifar da wani sabon kaura na dubban daruruwan jama’a daga gidajensu, tare da takaita zirga-zirgar kayan agaji, lamarin da ke kara fuskantar barazanar yunwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments