Babban malamin addini a kasar Iraki Aya. Ali Sistani ya yi allawadai da kisan da aka yiwa wasu yan kasar a tsakanin garuruwan Peshawar da Barajna a cikin yan kwanakin da suka gabata, wanda ya kai ga mutuwar mutane akalla 39.
Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta banalto ofishin Aya. Ali Sistani a birnin Najaf na kasar Iraki ya na fadar haka a jiya jumma’a. Sannan ya bukaci gwamnatin kasar Pakistan ta dauki matakan kare yan kasar wadanda ba su da wani wanda zai karesu sai ita.
Kafin haka dai wasu yan ta’adda wadanda suke riya kishin addini sun tsare motocin wasu musulmi wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa Pishawar, suka kashe da dama daga cikinsu.
Babban marja’in ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin kasar Pakistan da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hare haren da aka kaimasu.