Aya.Ahmad Khatami Ya Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da Aka Yi A Kasar Sudan

Limamin masallacin jumma’a a nan birnin Tehran ya yi allawadai da kissan kiyashin da ake yi a kauyukan kasar Sudan. Tashar talabjin ta Labarai a

Limamin masallacin jumma’a a nan birnin Tehran ya yi allawadai da kissan kiyashin da ake yi a kauyukan kasar Sudan.

Tashar talabjin ta Labarai a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubarsa ta biyu a sallar Jumma’an da ya jagoranta a jami’ar Tehran.

A yau kimani shekara guda Kenan da fara yakin cikin gida a kasar Sudan, wanda ya tilastawa miliyoyin mutane kaura daga gidajensu, sannan bayan haka ana binsu gida gida ana kashesu. Aya. Ahmad Khatami yayi kira ga bangarorin da suke rikici a kasar sudan su kawo karshen wahalar da suke jefa mutanen kasar a ciki.

A bangaren yakin neman zaben da ke gudana a kasar kuma, Aya. Ahmad Khatami ya yi kira ga yan takarar shugaban kasa kada su yi alkawula ga mutanen kasar da abubuwan da ba zai yu na. Ya ce kada su yi wa mutanen kasar alakawarin karya. Sannan yan takarar su bar bata juna a tsakaninsu.

Limamin ya yi kira ga mutanen kasar su fito don zaben shugabansu, don yin hakan- kamar yadda jagoran juyin juya halin musulunci ya fada- cika alhinin da mutanen kasar suka yi na rashin shugaba  Shahid Ra’isi da ministansa na harkokin waje shahida Dr Hussain Amir Abdullahiyan ne.

Aya. Khatimi ya bukaci mutane su zabi wanda suka ga yafi cancanta ya zama shugaban kasa a cikin mutane 6 da suke takarar neman shugabancin kasar. Ya kamala da cewa, su zabi wanda  ya fi kama da shugaban shahid Ra’isi a ra’ayinsa. 

Daga karshe limamin ya yi maganar muhimmancin ranakun farko na watan zulhajji, da kuma ranar Arafa. Ya kodaitar da mutane yin azumi da addu’o’ii a cikin dare da ranakun watan don samun lada mai yawa a wajen All..T..

Yansanda A Kasar Faransa Sun Kai Sumame A Cibiyar Munafukai Makiya JMI Wato MKO A Birnin Paris

A ranar laraban da ta gabata ce yansanda a birnin Paris na kasar Faransa suka kai sumame kan cibiyar munafukai makiya JMI ko MKO, inda suka gudanar da bincike a cikin gine ginen da suke cibiyar. Wadanda kuma suka hada da dakin ajiyar takardun ayyukan liken asiri da kuma dakin watsa labarai da radiyo da talabijin na kungiyar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta sami zantawa da wani wanda yake da masaniya kan abinda ya faru a ranar laraban da ta gabata, yana cewa. ‘Yansanda sun kwace dukkan takardun sirri da suka samu a hannun munafukan, wadanda mafi yawansu na liken asiri ne kan JMI, sun tafi da su. Sannan sun kama mutane uku daga cikin yayan wannan kungiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments