AU Ta Mika Sakon Ta’aziyya Ga Iran

Kungiyar tarayyar Afrika ta mika sakon ta’aziyyarta ga Iran, game da rasuwar shugaban kasar Ibrahim Ra’isi da kuma mukarabansa sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar

Kungiyar tarayyar Afrika ta mika sakon ta’aziyyarta ga Iran, game da rasuwar shugaban kasar Ibrahim Ra’isi da kuma mukarabansa sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

A cikin wata sanarwa Shugaban kwamitin kungiyar, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana matukar kaduwa da bakin ciki da labarin rasuwar Shugaban Kasa Seyeed Ibrahim Raïssi da Ministan Harkokin Waje, Dakta Hossein Amirabdollahian tare da abokan aikinsu a hadarin jirgin sama.

Mista Mahamat, ya mika sakon ta’aziyyarsa, juyayi da kuma goyon bayan kungiyar tarayyar Afirka ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci, Sayyid Ali Khamene’i, ga gwamnatin Iran da al’ummarta a wannan lokaci na radadi.

Kafin hakan dama shugabannin kasashen Afirka da dama sun bi sahun takwarorinsu na duniya wajen aikewa da sakonnin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Iran kan rasuwar Shugaba Ebrahim Raisi, bayan hadarin jirgin saman.

A sakonsa, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Iran kan rashin.

Shi ma Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya nuna jimami kan rasuwar.

Kasar Aljeriya ma ta tura sakon alhini, yayin da ita Masar, da Kenya, da Tanzania da kuma Morocco duk suka sun aike da sako na ta’aziyya kan rasuwar shugaban na Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments