APC Ta Amince Kan Cewa Manufofin Tinubu Sun Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kangin Talauci

Jam’iyyar APC mai mulki, ta amince da cewa manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun ƙara jefa al’ummar ƙasar nan cikin ƙangin talauci. Jaridar daily Trust

Jam’iyyar APC mai mulki, ta amince da cewa manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun ƙara jefa al’ummar ƙasar nan cikin ƙangin talauci.

Jaridar daily Trust ta bayar da rahoton cewa, Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na, Barrister Felix Morka ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.

Ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (Arewa maso Yamma), Salihu Mohammed Lukman martani.

Lukman, ya zargi APC da gaza cika alƙawuran da ta ɗaukar wa ’yan Najeriya, inda ya ce tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba su cika alƙawuran yaƙin neman zaɓensu ba.

Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyun adawa su haɗa kai su yi ƙoƙari wajen kawar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.

Amma yayin da yake martani, Morka, ya ce Shugaba Tinubu yana ɗaukar matakan gyara domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan da ya daɗe da lalacewa.

Sai dai ya ce gyaran da ake yi ya ƙara jefa al’umma cikin wahalhalun rayuwa.

A cewarsa, “Gwamnatin APC karkashin shugabancin Shugaba Tinubu tana daukar kwararan matakai domin gyara tattalin arziƙin kasar nan, inganta tsaro, da kuma kawo ci gaba mai ɗorewa.”

Ya ƙara da cewa rashin daukar irin wadannan matakai a gwamnatocin baya ne, ya jefa tattalin arziƙin ƙasar nan cikin mawuyacin hali na tsawon lokaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments