Cibiyar nazarin tattalin arziki da rayuwar zamantakewa ta ( shurish) ta fitar da wasu alkaluma da cibiyar tattara bayanai ta HKI ta fitar dake nuni da cewa; Daga fara kisan kiyashi a gaza a ranar 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu, wadanda suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya tun 1948 sun karu da kaso 42%.
Bayanin ya kuma cigaba da cewa rashin tsaro da matsaloli na siyasa ne suke ingiza mutane ficewa zuwa wasu kasashe, da hakan yake tattare da sakamako maras kyau ga ‘yan sahayoniya anan gaba.