An Zargi  Sojojin   Rwanda Da Kai Wa Fararen Hular Congo Hare-hare

Kungiyar kare hakkin dan’adam ta “Human Right Watch” ta zargi sojojin kasar Rwanda da kuma ‘yan tawayen M23 da  kai wa  fararen hular DRC hari.

Kungiyar kare hakkin dan’adam ta “Human Right Watch” ta zargi sojojin kasar Rwanda da kuma ‘yan tawayen M23 da  kai wa  fararen hular DRC hari.

A wani rahotonn da kungiyar kare hakkin bil’adam din ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata, ta ce;  Sojojin gwmanatin Rwanda da kuma ‘yan tawayen M23, sun rika kai wa fararen hula hari a tsawon wannan shekara ta 2024,musamma a sansanin ‘yan gudun hijira dake kusa da birnin Goma da shi ne babban birnin gundumar Kivu ta Arewa.

Ita ma MDD ta zargi sojojin na Rwanda da hada kai da kungiyar ‘yan tawaye ta M23, sai dai Kigali ta karyata zargin.

Rahoton na kungiyar kare hakkin bil’adan ya ce; tun a watan Janairu na wannan shekarar ne dai sojojin na Rwanda da kuma ‘yan tawayen na M23 suke kai wa sansanonin ‘yan gudun hijira hare-hare.

Fiye da mutane rabin miliyon ne rikice-rikice su ka tarwatsa a yankin Goma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments