An gudanar da gangami da tarurruka a yankuna daban daban na kasar Yemen a yau Jumma’a saboda goyon bayan da mutanen kasar suke bawa Falasdinawa a Gaza, wadanda sojojin HKI suke kashewa fiye da watanni 9 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa miliyoyin mutanen Yemen a yau Jumma, sun fito da ‘shi’arin “nasara ga Gaza’ a dandalin ’70 ‘da ke birnin San’aa babban birnin kasar da kuma wasu birane da garuruwa har kimani 200.
Labarin ya kara da cewa yankunan da mutanen kasar Yemen suka fita don taron goyon bayan mutanen Gaza sun hada da al-Hodeidah, Taiz, Ibb, Amran, Hajjah, Mahweet, Al-Jawf, Dhamar, Al-Dhale, da kuma Lahij.
Yau dai shi ne cikon jumma’a 40 a jere Kenan wanda mutanen kasar Yemen suke fitowa gangamin nuna goyon bayan Falasdinawa a Gaza. Wannan banda ayyukan soje wanda sojojin kasar suke yi don tallafawa falasdinawan. A cikin wannnan makon ne, a karon farko wani jirgin yaki mai kunan bakin wake, wanda kuma ake sarrafashi daga nesa ya kai hari cikin birnin Te’aviv babban birnin HKI, wanda ya sa jiragen samin yakin yahudawan suka maida martini da kona runbunan ajiyar makamashi na kasar Yemen dake birnin Hudaida