An Fara Gudanar Da  Zaman Juyayin Muharram A Najeriya

A cikin sassa-ssa mabanbanta na kasar Nigeria an fara gtudanar da zaman juyayin Muharram na shahadar Imam Husain ( a.s). A ranar Lahadin da ta

A cikin sassa-ssa mabanbanta na kasar Nigeria an fara gtudanar da zaman juyayin Muharram na shahadar Imam Husain ( a.s).

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka fara gudanar da zaman makokin na Imam Husain ( a.s) jikan manzon Allah ( s.a.wa) a garuruwan Abuja, Bauchi, Jos, kano, Potuskum da sauran garuruwa da biranen kasar.

A cikin tsohon birnin kano, Sheikh Sunusi Abdulkadir na Harkar Musulunci a karkashin Sheikh Ibrahim Zakzaki ya jagoanci zaman juyayin na  shahadar Imam Husain (a.s).

Za a cigaba da zaman na juyayin Ashura har zuwa ranar 10 ga Muharram  da ita ce ranar da Bani-Umayyah su ka kashe jikan ma’ainin Allah (s.a.w) tare da iyalansa  tsarkaka da sahabbansa managarta.

A kowace shekara, musulmi mabiya mazhabar Ahlul-Bayti (a.s) kan yi juyayin shahadar Imam Husain da ya faru a shekarar hijira ta 61.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments