An yi jana’izar Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas, a babban birnin Qatar Doha, taron janazar da ya samu halartar manyan jami’ai daga sassan yankin.
An binne gawar Haniyeh da aka nannade da tutocin Falasdinu a makabartar masarautar kasar da ke Lusail a arewacin Doha, Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad-Reza Aref da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Ali Baqeri Kani da sauran manyan baki da wakilai daga bangarorin Palasdinawa. .
Kafin haka dai, dubban masu zaman makoki da suka hada da wakilan kasashen duniya da dama sun gudanar da sallar jana’izar a babban masallacin birnin Doha, masallacin Imam Muhammad bin Abdul Wahhab, cikin tsauraran matakan tsaro.
An gudanar da addu’o’i da zanga-zangar yin Allawadai kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Gaza da yammacin kogin Jordan, tare da wasu kasashe da dama da suka hada da Jordan, Lebanon, Turkiyya, Yemen, Pakistan, Malaysia, da Indonesia Irakim Morocco, Tnunisia, Aljeriya da dai sauransu.