Amurka Ta Kakaba Wa Harkokin Man Iran Takunkumi

Amurka ta kakaba wasu sabbin takunkumai kan harkokin man fetur da sinadarai na Iran a matsayin martani ga harin ramuwar gayya da Jamhuriyar Musulunci ta

Amurka ta kakaba wasu sabbin takunkumai kan harkokin man fetur da sinadarai na Iran a matsayin martani ga harin ramuwar gayya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai a baya-bayan nan kan Isra’ila.

Ma’aikatar baitul malin Amurka a ranar Juma’a ta ce an tsara takunkuman ne da nufin kara matsa lamba kan Iran, gami da kayyade karfinta na samun kudaden shiga na makamashin da take amfani da shi don taimakawa masu gwagwarmaya a gabas ta tsakiya.

Ma’aikatar ta ce takunkumin nata ya shafi “kaso mai yawa” na jiragen ruwan da ke safarar man fetur da Iran ke fitarwa.

Sakatariyar baitul malin Amurka Janet L. Yellen ta bayyana cewa, “A matsayin martani ga harin da Iran ta kai wa Isra’ila, Amurka tana daukar kwararan matakai don kara dakile damar da gwamnatin Iran ke da shi na samar da kudade da kuma aiwatar da ayyukanta na tada zaune tsaye.”

Takunkumin na yau ya shafi kokarin Iran na samar da kudaden shiga daga masana’antar makamashinta da suka hada da bunkasa shirinta na nukiliya, da yaduwar makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka,” in ji ta.

Tun da farko sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Amurka ta kuduri aniyar takaita hanyoyin samun kudaden shiga na Iran saboda munanan ayyukanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments