Amurka Ta Gabatar Da Babbin Takunkumi Kan Kasar Iran A Kan Kera Makami Mai Linzami

Ma’aikatar Baitil Malin Amurka ta sanar cewa ofishin dake kula da kadarorin gwamnatin tana shirin kakakaba sabbin takunkumi kan wasu cibiyoyi dake Iran turkiya Oman

Ma’aikatar Baitil Malin Amurka ta sanar cewa ofishin dake kula da kadarorin gwamnatin tana shirin kakakaba sabbin takunkumi kan wasu cibiyoyi dake Iran turkiya Oman da kuma jamus  saboda da zarginsu da taimakawa kasar Iran wajen kera makami mai linzami na Balastic da shirin tan a nakiliya da kuma sauran tsare-tsaren da suka shafi tsaro.

Yace wadannan kafofi  kungiyar jihadi ta dakarunkare juyun musulunci na iran  da ma’aikatar tsaro da kuma bangaren kulada kayayyakin amfani soji da sauran kungiyoyin da Amurka ta sanya musu takunkumi,

Gwanatin Joe Biden wacce ke ikirarin yin amfani da diplomasiya wajen tunkarar kasar iran da kuma kokarin dawowa a tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran a shekara ta 2015 ba wai taki dawao wa cikin tattaunawar ba ne ta ci gaba da tsananta takunkumi ne ma kasar iran .

Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da kasar Iran ta sha nanata cewa tsare-tsarenta na soji da suka hada da kera makami mai linzami don tsaro ne da kare kai kuma baya cikin abubuwan da ake tattauanwa akai

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments