Bayanai daga Yemen na cewa sojojn Amurka na na Birtaniya sun sake kai wasu jerin hare hare ta sama a wasu sassa daban daban na kasar.
Tashar talabijin ta Al Masirah ta bayar da rahoton cewa, dakarun Amurka da na Birtaniya sun kaddamar da hare-hare a Sanaa babban birnin kasar Yemen, da lardin Amran da sauran yankunan kasar.
Jami’an Amurka sun tabbatar da kaddamar da hare-haren.
Sun ce sojojin Amurka sun kai hare-hare da yawa ta sama a kan “wuraren ajiyar manyan makamai na ‘yan Houthi wandanda da su a ake kai hari kan jiragen ruwa na soja da na farar hula da ke yawo a cikin tekun kasa da kasa a Tekun Bahar Maliya da na Aden”.
‘Yan Houthi da ke iko da arewacin Yemen, na cewa hare-haren na su na goyon bayan al’ummar Falasdinu ne dake fuskantar hare haren Isra’ila yau sama da shekara guda.