Amurka Ce Take Hana Shirin Tsagaita Wuta A Gaza Samun Nasara

Gwamnatin shugaba Biden tare da goyon bayanta wanda bai da iyaka ga HKI ne ya sa babu wani fatan samar da zaman alfiya a Gaza

Gwamnatin shugaba Biden tare da goyon bayanta wanda bai da iyaka ga HKI ne ya sa babu wani fatan samar da zaman alfiya a Gaza a cikin wani lokaci nan kusa.

Kamfanin dillancin labaran SAHAB na kasar Iran ya bayyana cewa a tarurrukan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza wadanda aka gudanar a biranen Doha na kasar Qatar da Alkahir na kasar Masar a baya-bayan nan, HKI ce take kawo wasu sharudda wadanda ya tabbatar kungiyar Hamas ba zata taba amincewa da su ba, don wargaza dukkan shirin tsagaita wuta a Gaza.

Kasar Amurka dai tana bayyana kanta a matsayin kasa wacce take bukatar sulhu a gabas ta tsakiya amma kuma itace take hana zaman lafiya samuwa a aikace. Saboda makaman da babu iyakan da take aikawa HKI da kuma goyon bayan siyasa da take bawa HKI ta ko ina. Kama daga majalisar dinkin duniya ko kuma a wasu wurare.

A cikin yan kwanakin da suka gabata ne sojojin HKI suka yi aikin soje na musamman a yankin yamma da kogin Jordan, aikin wanda ya dau kimani kwanai uku ya shafi garuruwan Jenin Ainushams da kuma Tulkaram.  A aikin sojen dai yahudawan sun kashe Falasdinawa da dama sun kuma lalata kayakin jama’a wadanda suka hada da wutan lantarki da ruwan sha.

Ministan harkokin wajen HKI Israel Katz ya bayyana dalilai na ayyukan sojen da cewa, HKI tana son  korar Falasdinawa gaba daya daga yankin. Wannan itace manufar HKI a Gaza ko kuma a yankin yamma da kogin Jordan da kuma gaza. Falasdinawa kimai miliyon 5 ne suke zaune a wadannan yankuna biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments