Amnesty: An Daure Sama Da Mutane 1000 Saboda Zanga-Zangar Yunwa

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International, ta bayyana cewa fiye da mutum 1,000 da suka yi zanga-zangar yunwa aka tsare a gidajen yari

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International, ta bayyana cewa fiye da mutum 1,000 da suka yi zanga-zangar yunwa aka tsare a gidajen yari daban-daban a Najeriya.

Kungiyar, ta zargi gwamnatin Nijeriya da kara matsa wa masu zanga-zangar lumana lamba ta hanyar gurfanar da fiye da 1,000 a kotu.

A ranar 6 ga watan Agusta, Sufeta-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama wasu daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin tada tarzoma, ciki har da waɗanda suka ɗauki nauyin ɗinka tutar Rasha.

A ranar Juma’a, Amnesty International ta sanar shafinta na X, cewa akwai bukatar a saki dukkanin waɗanda aka kama saboda yin zanga-zangar lumana ba tare da wani sharaɗi ba.

Kungiyar ta ce, “Gwamnatin Najeriya tana kara tsananta wa waɗanda suka yi zanga-zangar lumana kan yunwa.

“Sama da mutum 1,000 aka tsare a dukkanin faɗin kasar. A yau, an gurfanar da mutum 441 a kotun Kano, a wasu shari’o’i na rashin adalci da aka yi bisa tuhume-tuhumen ƙarya.‚

Amnesty International, ta kuma tunatar da gwamnatin Najeriya wajibcin kare haƙƙin ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma yin zanga-zangar lumana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments