Ambaliyar Ruwa A Saudiyya Ta Yi Sanadiyyar Hasarori Musamman a Birnin Madinah

Ambaliyar ruwa ta mamaye garuruwan Saudiyya tare da yin awungaba da tarin motoci Hotunan faifan bidiyo da ke yawo a kasar Saudiyya suna nuna yadda

Ambaliyar ruwa ta mamaye garuruwan Saudiyya tare da yin awungaba da tarin motoci

Hotunan faifan bidiyo da ke yawo a kasar Saudiyya suna nuna yadda ambaliyar ruwa take ci gaba da barna a kasar musamman yadda ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama mai karfi da ta afka wa unguwar Shahidai da ke birnin Madina mai alfarma, inda ta yi awon gaba da motoci da dama.

Cibiyar nazarin yanayi ta kasar Saudiyya ta yi gargadi kan mamakon saukan ruwan sama mai tsanani da illolin da ke tattare da shi, da iska mai karfi, da bullar yanayin sanyi mai tsanani, da kwararar ruwa a matsayin ambaliyar ruwa da cikan kwaruruka, kamar yadda kafar yada labaran Saudiyya ta bayyana.

Masu fafutuka a dandalin “X” sun yada faifan bidiyo a yammacin ranar Juma’a, inda suka nuna karfin mamakon ruwan sama da kuma kwararar da ke yi a “Unguwar Shahidai” da ke Madina, yana mamaye hanyoyi tare da yin awungaba da motoci.

Sun jaddada cewa: Ruwan sama kamar da bakin kwarya da mamakon ruwan sama ba a taba yin irinsa da irin wannan karfi ba, wanda suka bayyana a matsayin mahaukacin ruwa, inda ya kwashe duk wani abu da ke gabansa, da suka hada da gidaje da motoci, musamman a unguwar “Shahidai”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments