Ana ci gaba da gudanar da gagarumar zanga-zanga a kasashen yammacin Turai na neman kawo karshen “kisan kare dangi” a Gaza
Rahotonni suna ci gaba da bayyana yadda al’ummun kasashen yammacin Turai suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da kisan kiyashin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suke yi a Gaza, yayin da wasu kasashen Turai da Asiya suka gudanar da zanga-zangar neman a kawo karshen ta’asa kan Falasdinawa da kuma shigar da kayan agaji gare su cikin gaggawa.
A babban birnin kasar Denmark, Copenhagen, ya fuskanci wani gagarumin tattaki, inda masu zanga-zangar suka yi ta yawo a kan tituna, suna rera taken neman kawo karshen ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila cikin gaggawa, mahalarta zanga-zangar suna dauke da tutocin Falasdinu, suna masu kira da a gurfanar da shugabannin gwamnatin yahudawan sahayoniyya a gaban kotu a matsayin masu laifin yaki.
A yayin da dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a Berlin fadar mulkin kasar Jamus, inda masu zanga-zangar suka bukaci mahukuntan kasar da su daina duk wata hulda da jagororin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila, inda suka yi tir da gazawar kasashen duniya wajen ba da kariya ga al’ummar Falasdinu, tare da yin kira da a kawo karshen matakan wuce gona da iri, da killace al’ummar Falasdinu gami da shigar da agaji jin kai cikin hanzari gare su.