Al’ummar Zirin Gaza Sun Jaddada Aniyarsu Ta Ci Gaba Da Gwagwarmayar Duk Shahadan Sinwar

Al’ummar Falasdinu da ke Zirin Gaza sun jaddada cewa: Shahadar shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas Yahya Al-Sinwar ba za ta shafi gwagwarmayar Falasdinawa ba Falasdinawa

Al’ummar Falasdinu da ke Zirin Gaza sun jaddada cewa: Shahadar shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas Yahya Al-Sinwar ba za ta shafi gwagwarmayar Falasdinawa ba

Falasdinawa a Zirin Gaza sun bayyana cewa: Shahadar shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Yahya Al-Sinwar ba zai yi tasiri a kan gwagwarmaya a yankin ba, suna masu nuni da shahadar da dama daga manyan shugabanni a cikin ‘yan shekarun nan da suka gabata, ba tare da hakan ya janyo cikas ko rauni ga ‘yan gwagwarmaya ba.

A jawabai daban-daban da suka yi wa gidan talabijin na Aljazeera, Falasdinawa sun yaba da jajircewar da Sinwar ya nuna, da kuma samun shahadarsa a lokacin arangamar da ya yi da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya.

A ranar alhamis ce, haramtacciyar kasar Isra’ila kwatsam ta sanar da kisan Yahya Al-Sinwar, bayan da ya yi arangama da sojojinta, a wani gida da ke unguwar Tal al-Sultan a birnin Rafah da aka mamaye.

Sannan a ranar Juma’a, wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas Khalil Al-Hayya, a wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin ya sanar da shahadar Sinwar, ya kara da jaddada cewa kungiyar za ta ci gaba da bin tafarkinta na gwagwarmaya wajen yakar ‘yan mamaya har sai an fatattake su daga yankunan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments