Al’ummar birnin Jenin na Falasdinu sun gudanar da zanga-zangar yin tir tare da Allah wadai da kisan kiyashin makarantar Al-Ta’bi’een da yahudawan sahayoniyya suka yi a jiya Asabar
Al’ummar Falasdinu mazauna birnin Jenin da kewayensa sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a cikin daren jiya, inda suka yi tir tare da Allah wadai kan yadda sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu a Zirin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan lamarin da ke janyo kisan kiyashi kan Falasdinawa musamman mata da kananan yara a yankin.
An shirya zanga-zangar ce bisa gayyatar kungiyoyin Falasdinawa da na Musulunci, kuma mahalarta zanga-zangar sun yi ta tattaki a kan titunan birnin, suna rera taken yin Allah wadai da laifukan gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya musamman kisan kiyashin da take ci gaba da yi wa al’ummar Falasdinu a Zirin Gaza.
Mahalarta zanga-zangar sun yi kira da a samu hadin kai tsakanin kungiyoyin kasa da kasa wajen kalubalantar muggan laifuffukan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, tare da yin kira ga kasashen duniya da su shiga cikin lamarin cikin gaggawa domin dakatar da kai hare-hare da kuma ba da kariya ga al’ummar Falastinu.