Alkaluman Farko Suna Nuni Da Cewa Sake Gina Lebanon Yana Da Bukatar Dala Biliyan 3

Alkaluman da cibiyoyi mabanbanta su ka tattara ta hanyoyi daban-daban, yana nuni da cewa asarar da yakin na HKI ya hadda wa  Lebanon ta fuskar

Alkaluman da cibiyoyi mabanbanta su ka tattara ta hanyoyi daban-daban, yana nuni da cewa asarar da yakin na HKI ya hadda wa  Lebanon ta fuskar rusa gidaje ya dara na lokacin yakin 2006,musamman a unguwar Dhahiya dake kudancin Beirut.

A shekarar 2006 adadin gidajen da jiragen yakin HKI su ka rusa a  unguwar “Dhahiya” sun kai 246,amma a wannan yakin da bai kawo karshe ba, har a karshen Oktoba injinan yakin ‘yan sahayoniya sun rusa gidajen da su ka kai 220.

Asarar yakin tana karuwa a kowace rana bisa la’akari da munanan hare-haren na ‘yan sahayoniya suke kai wa  cikin birnin Beirut da kuma sauran garuruwan kudancin kasar ta Lebanon.

Wata kididdigar ta kuma nuna cewa a tsakanin gidajen zama da shagunan kasuwanci da hare-haren HKI su ka rusa zuwa yanzu sun kai 45,000, kaso 20% na wannan adadin gine-ginen kasuwanci ne.

Sake gina wadannan wuraren a matakin farko yana da bukatuwa da kwashe baraguzai masu yawa na gidajen da aka rusa, sannan kuma gyara wasu gidajen da aka illata ba tare da an rushe su baki daya ba.

A cikin birnin  Beirut da yankin Jabalu-Amil kadai adadin gidajen da aka rusa sun kai 7,000,kamar yadda kwamtin “Jihadul-Bina” mai kusanci da Hizbullah ya fadawa jaridar ‘al-akhbar ta Lebaanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments