Aljeriya Ta Ba Da Sanarwar Janye Jakadanta A Faransa Nan Take

Gwamnatin Aljeriya ta sanar da janyewar jakadanta a Faransa nan take. Ma’aikatar harkokin wajen kasar a cikin wata sanarwa da kamfanin dilancin labaren APS ya

Gwamnatin Aljeriya ta sanar da janyewar jakadanta a Faransa nan take.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar a cikin wata sanarwa da kamfanin dilancin labaren APS ya rawaito, ta ce daga yau Talata “mai kula da harkoki ne zai kula da al’amuran diflomatsiyya a kasarta faransa.

Tun a ranar 25 ga watan Yuli ne, Ma’aikatar Harkokin Wajen Aljeriya ta bayyana, a cikin wata sanarwa da ta fitar, da “rashin amincewa” da goyan bayan Faransa ga shirin cin gashin kai na Masarautar Maroko kan yankin yammacin Sahara.

Hakan dai a cewar wata majiya mai tushe ta Faransa, zai iya sa Aljeriya ta soke ziyarar da aka shirya shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune, zai kai a Paris a cikin watan Satumba mai zuwa.

Ita dai Faransa ta yi la’akari da cewa a halin yanzu makomar yammacin Sahara ya shiga cikin tsarin mulkin Moroko,” kamar yadda wata wasika da Emmanuel Macron ya aikewa Sarkin Morocco Mohammed VI, da kafafen yada labaren faransa suka samu samfarinta.

Yankin Yammacin Sahara, wanda kasar Spain ta yi wa mulkin mallaka, yana karkashin ikon Morocco ne, wadda ke ba da shawarar shirin cin gashin kai a karkashin ikonta.

Sai dai wannan yanki na da’awar ‘yan awaren Sahrawi na kungiyar Polisario, da ke samun goyon bayan Aljeriya, wadanda ke neman a gudanar da zaben raba gardama na cin gashin kai da aka shirya a lokacin tsagaita bude wuta a shekarar 1991.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments