Shugaban kungiyar Ansarallaha kasar Yemen Abdul-Malik al-Houthi ya jaddada cewa, Kungiyar za ta ci gaba da kai hare-hare kan “Isra’ila” da magoya bayanta domin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu da Lebanon.
Kalaman nasa sun zo ne a wani jawabi da ya yi wanda aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin na kasar Yemen, biyo bayan da jiragen yakin Amurka da Birtaniya suka kaddamar da hare-hare kan kasar Yemen, ciki har da babban birnin kasar Sanaa, inda ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar da yin amfani da jirgin yaki samfurin B-2 a karon farko a yankin.
Al-Houthi ya yi Allah-wadai da hare-haren ta sama tare da zargin Amurka da ba wa Isra’ila damar kai hare-hare a kasashen gabas ta tsakiya. “Washington na neman baiwa gwamnatin Tel Aviv damar mamaye yankin baki daya ta hanyar siyasa da tattalin arziki,” in ji shi.
Al-Houthi ya bayyana manufofin fadada “Isra’ila” a matsayin wata babbar barazana ba ga kasashen Larabawa kadai ba har ma ga daukacin yankin, yana mai kira ga ‘yan kasar Yemen da su yi zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa da al’ummar Lebanon.
Har ila yau ya zargi Amurka da hannu a yakin kisan kare dangi na “Isra’ila” a Gaza da Lebanon, yana mai cewa, “Amurka abokiyar gaba ce ta kowace ma’ana, kuma tana tare da gwamnatin sahyoniya a cikin laifuka da zalunci.”
Idan ba tare da goyon bayan Amurka ba, “Isra’ila” ba za ta iya ci gaba da yakin soji na tsawon wannan lokaci ba, in ji shi.
Al-Houthi ya yi nuni da irin ta’asar da ake yi a Gaza a matsayin shaida na zaluncin “Isra’ila” inda ya ba da misali da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take kai wa fararen hula hari da yunkurin hana abinci da ruwa isa arewacin Gaza.
Ya kuma jaddada cewa, hukumomin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya sun kasa dakatar da kisan kiyashin da ake yi, inda ya bukaci al’ummar musulmi da su tashi tsaye wajen yakar zaluncin Isra’ila.