Jiragen yakin HKI sun kai hare hare a waurare da dama a zirin Gaza a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata inda suka kashe Falasdinawa akalla 52.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa banda hare har ta sama sojojin yahudawan sun bude wutan Atilari a kan sansanonin yan gudun hijira da dama.
Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun tsananta hare hare kan Falasdinawa a Gaza ne sabota tilastawa kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa wadanda suke fafatawa da ita a Gaza, saboda su amince da duk abinda suka gabatar a shirin tattaunawar tsagaita wuta da ke gudana tsakanin biranin Doha na kasar Qatar da kuma Alkahira na kasar Masar.
Majiyar sojojin HKI ta tabbatar da cewa sun kai hare hare har sau akalla 24 a wurare daban daban a zirin Gaza.
Sannan majiyar hukumomi a Gaza ta bayyana cewa sojojin yahudawan sun kai hare hare a garuruwan Dayr-Al-Balah, Nusairat, haka ma sun kai hare hare atilary a kan anguwar Zaitun da Tel-hawa da kuma Shakoush a kusa da garin Rafah.
A wani labarin kuma kungiyar ‘Doctors Without Borders,’ ko MSF, ta bayyana cewa likitoci a Gaza suna cikin takura saboda yawan majinyata da ake kawo masu.