A wannan Litinin ce kasar Afrika ta kudu ke shigar da wani cikakken bayani akan “Isra’ila” a gaban kotun kasa da kasa (ICJ) wanda zai kara karfafa hujjar cewa Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Falasdinu.
Wata majiyar ofishin jakadancin Afirka ta Kudu da ba a bayyana sunanta ba ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa za a gabatar da taron ne a wannan Litinin.
Ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Ronald Lamola ya shaidawa jaridar Daily Maverick cewa, karin shaidar a hankalce ya tabbatar dalla-dalla cewa “wannan ba wai kawai batun kisa ba ne, batu ne na kisan kiyashi.”
A cewar rahoton, da zarar an gabatar da wannan bayani, “Isra’ila” tana da har zuwa ranar 28 ga Yuli na shekara mai zuwa don kare kanta dangane da hakan.
A cikin watan Janairu, kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da hurumin daukar matakin gaggawa da kasar Afirka ta Kudu ke nema a shari’ar da ta ke yi kan ayyukan “Isra’ila” a yakin Gaza.
Duk da bukatar da Isra’ila ta gabatar na korar karar da yin watsi da ita, kotun duniya ta ce ba za ta yi watsi da karar ba.
Kotun ta ICJ ta ba da umarnin cewa wasu hakokin da Afirka ta Kudu ta gabatar a shari’ar kisan kiyashin Isra’ila a Gaza abin dubawa ne da kyau.
Kasashe da dama sun bi sahun Afirka ta kudu, daga cikinsu akwai Turkiyya, Nicaragua, Falasdinu, Spain, Mexico, Libya, Bolivia, da Colombia.
A yayin da ake ci gaba da sauraren karar, kotun ta amince da hakkin Falasdinawa a Gaza na a kare su daga aikata kisan kiyashi a kansu.
Daga cikin matakan da Afirka ta Kudu ta nema, akwai dakatar da kai hare-haren wuce gona da iri, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa kusan 43,000.