Afirka ta Kudu ta yi Allah wadai da cin zarafi da Isra’ila ke yi wa Labanon

Afirka ta Kudu ta yi Allah wadai da harin bam da Isra’ila ta kai kan kasar Labanon tare da yin kira ga kasashen duniya da

Afirka ta Kudu ta yi Allah wadai da harin bam da Isra’ila ta kai kan kasar Labanon tare da yin kira ga kasashen duniya da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da su yi aiki bisa ka’idojin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu ta fitar ta bayyana cewa, harin da Isra’ila ta kai kan kasar Labanon babban cin zarafi ne ga yankin kasa mai cin gashin kanta da kuma keta dokokin kasa da kasa.

Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a tsakiyar birnin Beirut, a ranar 10 ga watan Oktoba, inda fararen hula 22 suka yi shahada tare da raunata fiye da 117, tana mai bayanin cewa “Isra’ila ta kai Hare-hare da makamai masu linzami a wata unguwa mai yawan jama’a da gine-gine da kananan shaguna a tsakiyar birnin Beirut babban birnin kasar.”

Bayanin Ya kara da cewa, “Dole ne kasashen duniya da kwamitin sulhu na MDD su ci gaba da kare dokokin kasa da kasa da dokokin jin kai.”

Sannan bayanin ya yi kira da a gaggauta kawo karshen tashin hankalin, domin yayin da ake ci gaba da ci gaba da gwabzawa, za a kara fuskantar barazanar fadawa cikin wani babban rikici na soji, wanda ke zama babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments