Adadin Falasdinawa da da suka yi shahada tun fara kai hare-haren sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba ya karu zuwa 37,431 kuma wadanda suka jikkata zuwa 85,653, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta tabbatar.
A cikin rahotonta na yau da kullun, ma’aikatar lafiya ta bayyana cewa, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata sojojin mamaya na Isra’ila sun kashe mutane 101 tare da jikkata wasu 169 na daban.
An yi nuni da cewa yawancin wadanda abin ya shafa na ci gaba da zama a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, saboda motocin daukar marasa lafiya da jami’an agaji na farar hula ba su iya isa gare su.
Rahoton tashar Almayadeen ya ce; sojojin mamaya na Isra’ila sun sake yin wani kisan kiyashi ta hanyar kai hari a wani yanki a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Shati da ke yammacin Gaza.
Tun da farko wakilin Al Mayadeen a Gaza ya rawaito cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a yammacin Rafah da ke kudancin zirin Gaza. Har ila yau jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan garin Aabasan al-Kabira da ke gabashin Khan Younis a kudancin Gaza.