Adadin Falasdinawan Da Sukayi Shahada Sanadin Hare-haren Isra’ila Ya Zarce 40,000

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce adadin mutanen da sukayi shahada sanadin, kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza ya zarce 40,000. A rahotonta na baya-bayan

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce adadin mutanen da sukayi shahada sanadin, kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza ya zarce 40,000.

A rahotonta na baya-bayan nan kan wadanda suka mutu da aka fitar ranar Alhamis, ma’aikatar ta ce an kashe mutane 40 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu tun daga ranar 7 ga Oktoba zuwa 40,005. Yawan wadanda suka jikkata kuma ya haura 92,400.

Jami’an tsaron farar hula sun ce adadin na gaskiya zai fi haka idan aka yi la’akari da yadda wasu gawarwakin da dama suka rage a karkashin baraguzan gine-ginen da Isra’ila ta jefa bama-bamai.

A watan Yuli, Lancet, wata babbar jarida ta likita, ta kiyasta cewa adadin wadanda suka mutu zai iya zama 186,000 ko ma fiye.

Lancet ta ce adadin ya hada da mutuwar kai tsaye da kuma wadanda har yanzu ke binne a karkashin baraguzan ginin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments