A Kalla Mutane 4 Ne Su Ka Yi Shahada A Wani Hari Da HKI Ta Kai A Birnin Beirut

Rahotanni da suke fitowa daga birnin Beirut sun ambaci cewa jiragen yakin HKI sun kai hari da makamai masu karfin fashewa akan wani gini dake

Rahotanni da suke fitowa daga birnin Beirut sun ambaci cewa jiragen yakin HKI sun kai hari da makamai masu karfin fashewa akan wani gini dake tsakiyar birnin Beirut.

Tashar talabijin din ‘al-mayadin’ ta bayyana cewa; Jiragen  yakin HKI sun harba makamai masu tsananin karfi akan wani gini  mai hawa takwas dake unguwar ‘Basdha” a birnin Beirut da hakan ya yi sanadiyyar rushewar ginin  baki daya.

Rahoton tashar talabijin din ya kuma ce; ginin da aka kai wa harin yana cike da fararen hula, kuma sauran gine-ginen da suke kusa da shi duk sun illata.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta ce, bayanan farko suna nuni da cewa mutane 4 ne su ka yi shahada, kuma wasu 23 sun jikkata.

Har yanzu ana cigaba da zakulo mutanen da suke a karkashin baraguzan ginin da ya zube kasa baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments