Somalia ta soki furucin Burtaniya Kan ballewar Somaliland daga kasar

Ministan harkokin wajen Somalia Ahmed Moalim Faki Ahmed, ya soki kalaman jakadan Burtaniya a kasar, Mike Nithavrianakis, inda ya yi ishara da ballewar yankin “Somaliland.”

Ministan harkokin wajen Somalia Ahmed Moalim Faki Ahmed, ya soki kalaman jakadan Burtaniya a kasar, Mike Nithavrianakis, inda ya yi ishara da ballewar yankin “Somaliland.” Tare da bayyana hakan a matsayin katsalandan a cikin harkokin Somalia da hadin kanta ,  yana mai jaddada cewa “ba za a amince da haka ba.”

Ministan harkokin wajen Somaliya, Ahmed Moalim Faki Ahmed, ya yi kakkausar suka ga jakadan Burtaniya a Somaliya, Mike Nithavrianakis, tare da bayyana kalaman nasa a matsayin “kai hari a kan ‘yanci da hadin kan Somaliya.”

Rikicin diflomasiyyar ya taso ne bayan Nithavrianakis ya ce, a cikin wani sakon da ya rubuta a kan shafinsa na dandalin “X”, cewa Birtaniya “tana alfahari da tallafawa ayyukan ban mamaki da HALO Trust ke yi a Somalia da Somaliland,” wanda ministan Somaliya ya jaddada cewa furta hakan na nufin amincewa ne da raba kasar Somalia.

Faki Ahmed ya jaddada cewa “raba hadin kan kasa da kuma raba ta da sunaye daban-daban guda biyu, ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma hakan yana zaman wata mummunar matsaya ta Burtaniya kan ‘yancin kai da hadin kan Somaliya.”

Abin lura shi ne cewa kungiyar “Halo Trust” kungiya ce da ke da hedkwata a kasar Birtaniya, kuma ta shahara wajen aikin kawar da ma’adanai da kuma kawar da bama-bamai, a yankin “Somaliland” da kuma kudancin kasar tun 1999.

Bayanin na ministan harkokin wajen Somaliya ya nuna kwakkwaran matsayar gwamnatin Somaliya kan batun yankin “Somaliland”, wanda ya ayyana ballewarsa daga Somaliya a shekarar 1991, amma har yanzu ba a amince da shi a matsayin kasa a hukuamnce a duniya ba, kuma gwamnatin Somaliya tana daukarsa a matsayin wani muhimmin bangare na kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments