Pakistan Ta Shelanta Doka Ta Baci Saboda Bullar Cutar Kendanbiri A Kasar

Firai ministan kasar Pakistan ya shelanta doka ta baci a duk fadin kasar bayan an tabbatar da bullar cutar kendar-biri a kasar. Kamfani dillancin labaran

Firai ministan kasar Pakistan ya shelanta doka ta baci a duk fadin kasar bayan an tabbatar da bullar cutar kendar-biri a kasar.

Kamfani dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto firai ministan kasar Shehbaz Sharif  yana fadar haka bayan kammala wani taro na musamman don tattauna kan yadda za’a hana cutar yaduwa a kasar.

Mai Magana da yawun ofishin firai ministan kasar na Pakistan ya bayyana cewa bayan taron gaggawa, wanda firai ministan ya kira, don tattauna batun da jami’an gwamnatinsa wadanda abin ya shafa, ya bada sanarwan cewa ma’aikatar kiwon lafiya a kasar ta gano mutane 11 dauke da cutar ta kendan biri a kasar, ya kuma kara da cewa al-amarin bai yi kamada cutar korona ba, don ana iya shawo kanta da gaggawa idan an dauki matakan da suka dace.

Labarin ya kara da cewa bayan da MDD ta bada sanarwan bullar cutar a kasashe da dama a duniya, Islamabad ta dauki matakin karfafa bincike a hanyoyin shiga kasar, wadanda suka hada da tashoshin jiragen sama da kuma kaniyakokin kasar ta kasa da ruwa. Ya kara da cewa za’a samar da kayakin aikin gwaje-gwajen cutar a tashoshin jiragen sama na kasar don gano fasinjoji da suka fito daga yankin gabas ta tsakiya masu dauke da cutar.

Cutar kendar biri dai ta bulla a cikin watan Yulin shekara ta 2022 har zuwa watan Mayun shekara 2023, a lokacinda dai mutane 90,000 suka kamuj da ita, inda 140 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

Ana daukar cutar kendanrbiri ne daga dabbobi da kuma haduwa da wanda yake dauke da cutar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments