Tawagar Iran, Ta Ciri Tuta A Gasar Duniya Ta Fasahar Kirkirar Mutum-Mutumi

Tawagar daliban Iran ta ciri tuta a gasar duniya ta fasahar kirkirar mutum-mutumi ko robotic inda ta yi nasarar lashe kyautar azurfa. An gudanar da

Tawagar daliban Iran ta ciri tuta a gasar duniya ta fasahar kirkirar mutum-mutumi ko robotic inda ta yi nasarar lashe kyautar azurfa.

An gudanar da gasar ce bana a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, a tsawon kwanaki uku daga ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2024.

A cewar Parstoday, a yayin wannan gasa, tawagar daliban kasar Iran ta robotics da ta kunshi ‘yan shekaru 7 zuwa 17, da suka kunshi fitattun dalibai 48, sun shiga gasar a bangaren wassanni na rugby, kwallon kafa, da kere-kere inda ta samu lambar yabo ta azurfa.

A baya, tawagar daliban kasar Iran ta samu matsayi na uku a gasar duniya ta shekarar 2019 da aka gudanar a kasar Malaysia, matsayi na biyu a gasar duniya ta shekarar 2022 a kasar Indiya, sannan kuma a gasar ta 2023 da aka yi a kasar Sin.

Haka kuma, a shekarar da ta gabata, matasan kasar Iran sun zama zakaru a gasar Asiya a Malaysia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments