WHO, Na Nazarin Ayyana Cutar Kyandar Biri A Matsayin Mai Hadari A Duniya  

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana damuwa kan yaduwar sabon nau’in cutar kyandar biri, da yanzu haka ke saurin yaduwa

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana damuwa kan yaduwar sabon nau’in cutar kyandar biri, da yanzu haka ke saurin yaduwa a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo.

Mista Tedros Adhanom ya tabbatar da cewa zai karbi shawara a yau don ganin ko za a ayyana cutar a matsayin mai matukar hadari a fadin duniya.

Cikin jawabin da ya gabatar a farkon taron gaggawa da Hukumar ta yi, ya ce a shekarar da ta gabata an samu karuwar wadanda cutar ta kama, sannan kuma yawan wadanda suka kamu a shekarar da muke ciki ma ya zarta na bara da dubu 14, sannan an samu mace-mace 524.

Dr Tedros, ya ce a watan daya wuce kadai an samu wadanda suka kamu da sabuwar nau’in cutar a kasashe kamar Burundi da Kenya da Rwanda da kuma Uganda, inda a bara ba a samu bullar cutar ba.

Hukumar Lafiya ta Duniyar ta fara shirin daukar mataki kan cutar a nahiyar Afirka, inda take bukatar dala miliyan 15 domin lura da yaduwa da kuma shiryawa cutar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments