Kasar Chana Ta Jaddada Hakkin Iran Na Kare Mutuncin Kasarta Da Kimar Al’ummarta

Kasar Chana ta tabbatar da hakkin Jamhuriyar Musuluncita Iran na kare mutuncinta, tsaro da kuma martabarta ta kasa A wata tattaunawa da ta gudana ta

Kasar Chana ta tabbatar da hakkin Jamhuriyar Musuluncita Iran na kare mutuncinta, tsaro da kuma martabarta ta kasa

A wata tattaunawa da ta gudana ta hanyar wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen kasar Chana Wang Yi da takwaransa na Iran Ali Baqiri Kani, Wang Yi ya bayyana cewa: Chana tana goyon bayan ‘yancin da Iran ke da shi na kare mutuncin kasarta, tsaro da kuma martabarta.

Wang ya jaddada yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh a birnin Tehran a ranar 31 ga watan Yuli, inda ya maimaita cewa, kisan Haniyeh ya shafi shirin tsagaita bude wuta kai tsaye tare da raunana zaman lafiyar yankin.

Wang Yi ya kuma kara da cewa, kasar Chana tana goyon bayan Iran wajen kare ikonta, tsaro, da martabarta bisa doka da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kuma a shirye take ta kulla alaka ta kut da kut da Iran.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ke gudanar da atisayen soji a yankunan yammacin kasar da za a ci gaba da yi har zuwa ranar Talata, don haɓaka shirye-shiryen yaƙi da kuma fadaka kan halin da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments