Pezeshkian: Siyasar Amurka Ta Harshen Damo Ce Ke Karfafa Isra’ila Wajen Aikata Laifuka

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce manufofin siyasar harshen damo ta Amurk da wasu kasashen Turai sun kara karfafa gwiwar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila 

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce manufofin siyasar harshen damo ta Amurk da wasu kasashen Turai sun kara karfafa gwiwar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila  wajen aikata munanan laifuka a Gaza da kuma yankin gabas ta tsakiya.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel, Pezeshkian ya ce a yanzu komai a fili yake ga kowa kan cewa, gwamnatin Isra’ila ita ce ke yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin gabas ta tsakiya da kuma tsaro na kasa da kasa.

Ya kara da cewa “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya,  kuma ta yi imanin cewa ya zama wajibi kan dukkanin bangarori na kasa da kasa su dakatar da duk wani yanayi na shishigi da barazana ga zaman lafiyar duniya.”

Pezeshkian ta bayyana hakan ne kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wa wata makaranta a gabashin zirin Gaza hari, inda dubban Falastinawa suke samun mafaka bayan da Isra’ila ta raba su da muhallansu, harin da ya yi sanadin shahadar mutane fiye da 120, da kuma jikkata wasu da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments