Unicef: A Duk Kwanaki Biyu “ Isra’ila” Tana  Kashe Karamin Yaro Daya

Asusun Kananan yara na MDD “ Unicef” ya sanar da cewa adadin kananan yaran Falasdinawa da suke mutuwa ya karu da kaso 250% idan aka

Asusun Kananan yara na MDD “ Unicef” ya sanar da cewa adadin kananan yaran Falasdinawa da suke mutuwa ya karu da kaso 250% idan aka kwatanta da gabanin 7 ga watan Oktoba na 2023.

A cikin wani bayani da Asusun Kananan yaran ya fitar a jiya Litinin ya ce; Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu  akwai kananan yara 143 da su ka yi shahadai a yammacin kogin Jordan kadai.”

Har ila yau sanarwar ta ce; A cikin duk kwanaki biyu HKI tana kashe karamin yaro Bafalasdi ne daya wanda hakan ya fara ne tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Babbar jami’ar zartarwa ta kungiyar “ Unicef” Kathrine Russell ta ce; A cikin shekaru masu tsawo, kananan yara a yankin yammacin Kogin Jordan suna rayuwa a cikin tashin hankali da  firgici, sai dai bayan barkewar yakin Gaza, al’amurra sun kara tabarbarewa a yankin.

Har ila yau Russell ta yi ishara da cewa, rabin yaran da aka kashe suna a yankunan Jenin da Tul-Karam da Nablus, domin a cikin shekaru biyu na bayan nan wadannan yankunan sun fuskanci karuwar tashe-tashen hankula. Haka nan kuma ta ambaci wani adadi na kananan yaran da sun kai 440 da aka jikkata ta hanayar harbinsu kai tsaye da albarusai.

Russell ta yi kira da a kawo karshen yaki yanzu ba tare da bata lokaci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments