Pezeshkian, Ya Yi Fatan Karfafa Alaka Da Kasashen Larabawa A Yankin

Zababben shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya yi kira ga kasashen Larabawa na yankin da su shiga “tattaunawa mai ma’ana” da kuma kokarin hadin gwiwa

Zababben shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya yi kira ga kasashen Larabawa na yankin da su shiga “tattaunawa mai ma’ana” da kuma kokarin hadin gwiwa tare da Iran don inganta hadin kai, tsaro, da wadata a fadin yankin.

Pezeshkian ya yi wannan tsokaci ne a cikin wani ra’ayi mai taken “Together, for a Strong and Probled Region”, wanda aka buga a jaridar Al-Araby Al-Jadeed da ke birnin Landan a ranar Laraba.

“A shirye nake da ‘yan uwana makwabta a yankin domin mu dauki matakai tare da bin hanyar tattaunawa mai ma’ana da inganta hadin gwiwa da hadin kai tsakanin kasashe da gwamnatocin yankin,” in ji shi.

Pezeshkian ya yi kira ga dukkan kasashen yankin da su yi aiki don ” aza harsashin ginin wani yanki mai karfi”.

“Ina mika hannun abota da ‘yan uwantaka zuwa ga dukkan makwabtan yanki domin cimma wannan buri,” in ji zababben shugaban kasar ta Iran.

Pezeshkian ya jaddada cewa, Iran da kasashen Larabawa da na musulmi makwaftanta ra’ayi daya ne, kuma suna da muradu daya da suka shafi batutuwa da dama da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da ra’ayin cewa tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin ya ta’alaka ne da amincewa da hakkokin al’ummar Falastinu na tsayin daka na adawa da mamaya, don samun ‘yancin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments