Shugaban Najeriya Ya Kara Samun Wa’adin Jagorantar Kungiyar ECOWAS

An sake zabar shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasasen yammacin Afirka. An sake zabar Tunubu, a wannan mukamin ne

An sake zabar shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasasen yammacin Afirka.

An sake zabar Tunubu, a wannan mukamin ne a yayin taron shugabannin kungiyar karo na 65, da ya gudana a Abuja, fadar mulkin Najeriya a ranar Lahadi.  

Da yake jawabi, shugaba Tinubu ya bukaci mambobin Ecowas su mayar da hankali wajen bayar da gudunmuwar su ta fannin kudaden gudanarwar kungiyar wanda ake amfani dasu wajen yaki da ayyukan ta’addanci.

Tun da farko a ranar Lahadin, hukumar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, Ecowas ta yi gargadin cewa yankin, zai iya wargajewa bayan da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar dake karkashin mulkin soji suka sanar da ficewar su daga kungiyar.

Shugaban hukumar, Omar Touray, matakin da kasashen uku suka dauka barazana ce ga kungiyar mai shekara hamsin.

Ya ce kafa wata sabuwar kungiya zai iya kawo cikas ga huddar kasuwanci marar shinge, da kuma zirga-zirga a tsakanin mutane miliyan dari hudu na yankin.

Kasashen uku na sahel, dake kalkashin mulkin soji, wato Mali, Burkina Faso, da kuma Nijar, sun jadadda a ranar Asabar cewa ba su ba komawa cikin kungiyar ta ECOWAS.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments