Al-Houthi Ya Bukaci Hadin Kan Al’ummar Musulmi Domin Kaucewa Kiyayar Da Ake Nunawa Yemen

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yaman ya bukaci hadin kan musulmi, inda ya yi nuni da cewa, kasashe da dama ba su shiga cikin tarkon

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yaman ya bukaci hadin kan musulmi, inda ya yi nuni da cewa, kasashe da dama ba su shiga cikin tarkon da kawancen da Amurka ke jagoranta na yaki da kasar Yemen ba, har ma suna da hadin kai kai tsaye da kasar Yemen a maimakon haka.

Jagoran na kungiyar ta Ansarullah, Abdel Malik Al’Houthi, Al-Houthi ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, a cikin wani jawabinsa inda ya ci gaba da cewa: “Babbar gazawar Amurka ita ce ta kasa hada kasashen da ke makwaftaka da tekun Maliya a ayyukan da suke yi na tallafa wa Isra’ila, haka nan Amurka ta gaza tilasta wa Larabawa da kasashen da ke makwabtaka da ita wajen kai mana hari daga kasashensu. “

Ya ce har yanzu Amurka na kokarin yin amfani da Saudiyya wajen matsa wa kasar Yemen lamba, yana mai jaddada cewa, “Amurka ta aiko mana da sakwannin da za su tilasta wa Saudiyya daukar matakai na kiyayya, a halin yanzu.”

Ya kuma gargadi Riyadh game da hada baki da Amurka, da Burtaniya, da gwamnatin Isra’ila wajen kiyayya da Yemen.

Al-Houthi ya dauki duk wani mataki da Saudiyya za ta dauka kan kasar Yemen a matsayin amfanar Isra’ila da Amurka kuma ya ce “Mun yi gargadi ta hanyar masu shiga tsakani, kuma mun ba da shawarar cewa Saudiyya ta kaucewa wanan, Amurka na da niyyar shigar da kasar Saudiyya cikin yakin da take yi da mu, wanda kuma hakan zai haifar da babban tashin hankali.”

https://iranpress.com/yemen-s-ansrullah-warns-saudi-arabia-against-colluding-with-us–uk

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments