Iran: Shugabannin Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Aike Wa Pezeshkiyan Da Sakonnin Taya Murna

Bayan nasarar da Masoud Pezeshkian ya samu a zaben shugaban kasar Iran zagaye na biyu, jami’ai da shugabannin kasashe daban-daban na dniya suna ci gaba

Bayan nasarar da Masoud Pezeshkian ya samu a zaben shugaban kasar Iran zagaye na biyu, jami’ai da shugabannin kasashe daban-daban na dniya suna ci gaba da aike masa da sakonni na taya shi murnar nasarar da ya samu.

Ivan Gil, ministan harkokin wajen Venezuela, a cikin wata sanarwa da aka watsa a dandalin X,  ya taya Iran murnar zaben shugaban kasa karo na 14 da aka gudanar cikin nasara.

Sayyid Ammar Hakim, shugaban jam’iyyar  Hikmat ta kasar Iraki, yayin da yake taya Masoud Al-Madijian murnar nasarar lashe zaben sabon shugaban kasa, ya taya shugabanni da al’ummar Iran da kuma gwamnatin Iran murnar nasara ta sabuwar demokradiyya a zaɓen shugaban kasar Iran.

“Mohammad Shehbaz Sharif”, Firayim Ministan Pakistan, ya sanar a yau a cikin sakon taya murna: “Ina mika sakon taya murna ga dan uwana Dr. Masoud Pezeshkiyan bisa nasarar lashe zaben shugaban kasar Iran.”

Shehbaz Sharif ya jaddada cewa: Ina fatan yin aiki kafada da kafada da zababben shugaban kasar, Dr. Pezeshkiyan, domin kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen Iran da Pakistan, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Shi ma a nasar bangaren Ayaz Sadiq shugaban majalisar dokokin Pakistan ya taya Masoud Pezeshkian murnar nasarar zaben shugaban kasar Iran karo na 14.

Shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev a cikin sakonsa na yau, ya taya Masoud Pezeshkiyan murnar lashe zaɓen sabon shugaban ƙasar Iran, inda ya rubuta cewa: Muna godiya da alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Azarbaijan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda ta ginu a kan ginshikai masu karfi kamar tushen addini da al’adu, abokantaka da ‘yan uwantaka .

Massoud Pezeshkiyan ya zama zababben shugaban al’ummar kasar ta hanyar lashe mafi yawan kuri’u a mataki na biyu na zaben shugaban kasa karo na 14.

A cewar sanarwar Mohsen Eslami, kakakin hedkwatar zaben kasar, daga cikin mutane miliyan 61 da dubu 452 da 321 da suka cancanci kada kuri’a, mutane miliyan 30 da dubu 530 da 157 ne suka halarci zaben, wato kashi 49 da 8 cikin dari.

Masoud Pezeshkian ya lashe zaben shugaban kasar Iran karo na 11 da kuri’u miliyan 16 da dubu 384 da 403.

Saeed Jalili, dan takara da ya tsallake zuwa zagaye na biyu na zaben, ya samu kuri’u 13,538,179.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments