Colombia Za Ta Dakatar Da Fitar Da Gawayi Zuwa Isra’ila Muddin Yakin Gaza Ya Ci Gaba  

Shugaban Colombia Gustavo Petro ya sanar a ranar Asabar cewa kasarsa za ta dakatar da fitar da gawayi zuwa Isra’ila muddin aka ci gaba da

Shugaban Colombia Gustavo Petro ya sanar a ranar Asabar cewa kasarsa za ta dakatar da fitar da gawayi zuwa Isra’ila muddin aka ci gaba da yaki a zirin Gaza.

“Za mu dakatar da fitar da gawayi zuwa Isra’ila har sai ta dakatar da kisan kiyashi,” in ji shugaban a dandalin sada zumunta.

Dama a watan Mayu ya sanar da yanke huldar diflomasiyya da Isra’ila, yana mai bayyana gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu ta “kisan kare dangi” a yakin da take yi a zirin Gaza.

Tuni da ma Mista Petro yake caccakar Firaiministan Benjamin Netanyahu sannan ya yi kira ga Afirka ta Kudu ta saka shi a cikin karar da ta kai Isra’ila a kotun duniya kan zarginta da kisan kare-dangi a Gaza.

Ya fada a waccen lokacin cewa ”Mun yanke huldar jakadanci da Isra’ila…saboda kasancewarta gwamnati da shugaban kasa masu kisan kare-dangi,” kamar yadda ya fada a yayin da yake jawabi ga dandazon jama’a a Bogota, don tunawa da Ranar Ma’aikata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments