Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jagorancin Juyayin Cika Shekaru 35 Da Rasuwar Imam Khumaini {r.a}

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba za su taba mance mummunan tasirin harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsa

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba za su taba mance mummunan tasirin harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsa ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsa ya yi mummunar illa ga yahudawan sahayoniyya, kuma a sakamakon wannan hari ne yahudawan sahayoniyya suka birkice tare da shiga cikin mummunan tashin hankali da kuma dimuwa da ba za su taba shiga ba, kuma ba za su taba farfadowa daga gare shi ba.

A farkon jawabinsa na yau litinin a wajen taron juyayin cikan shekaru 35 da rasuwar Imam Khumaini (r.a), Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabo batutuwa da suka shafi al’ummar musulmi, Falasdinu da shahadar shugaban kasar Iran da mukarrabansa, inda ke bayyana cewa: A mahangar Imam Khumaini batun Falasdinu yana daya daga cikin batutuwa mafiya muhimmanci don haka ya sanya shi cikin batun farko a duniya, yana mai jaddada cewa: A yanzu abin da marigayi Imam ya yi hasashe kan makomar Falasdinu yana tabbata.

Jagoran ci gaba da cewa: Batu na biyu kuma shi ne al’amarin da ya faru mai daci da rashin abin kauna shugaban kasar Iran, kuma wannan lamari ne babba mai girman tasiri a cikin kasa da kuma fadin duniya.

Sannan Jagoran ya tabo batu na uku da cewa: Imam Khumaini ya rubuta wasika zuwa ga tsohon shugaban tarayyar Soviet cewa, Yana jin kashin mulkin gurguzu yana karyewa, kuma wannan lamari ya faru kowa ya ganshi a tarihi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments