Ministan Harkokin Cikin Gidan Iran: Tunanin Imam Khumaini {r.a} Ya Zama Abin Koyi Ga Al’ummar Duniya

Ministan Harkokin Cikin Gidan Iran ya ce: Tunanin Imam Khumaini {r.a} ya zama abin koyi mai kima ga dukkan al’ummar duniya masu ‘yanci Ministan harkokin

Ministan Harkokin Cikin Gidan Iran ya ce: Tunanin Imam Khumaini {r.a} ya zama abin koyi mai kima ga dukkan al’ummar duniya masu ‘yanci

Ministan harkokin cikin gidan kasar Iran Ahmed Vahidi ya jaddada a cikin sakonsa na tunawa da cika shekaru talatin da biyar da rasuwar Imam Khumaini (r.a) cewa: Tunanin Imam Khumaini ya zama abin koyi mai kima ga dukkanin al’ummar duniya masu ‘yanci. Wahidi yana mai jaddada cewa: Gwagwarmayar marigayi Imam Khumaini ta tabbatar wa al’ummar musulmi wani misali na alkawarin da Allah ya yi na ‘yantar da wadanda ake zalunta daga kangin rauni da kuma ba su iko a kan doron kasa. Don haka tunanin Imam Khumaini bai takaitu ga Iraniyawa kawai ba, saboda tunani ne na neman ‘yancin kai da daukakan dukkanin al’ummar musulmi da ‘yantattun al’ummar duniya, kamar yadda a yau ake ganin tasirin wannan tunani na nuna adawa ga zalunci a wurare masu nisa na duniya kan kisan kiyashin da yahudawan sahayoniya suke yi a zirin Gaza, da kuma mafi tsananin tattakin da aka yi a ranar Qudus ta duniya, sakamakon haka tunanin marigayi Imam Khumaini karfafa yunkurin dan Adamtaka ne da na Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments