Ana Sa Ran Kimanin Motocin Agaji 200 Su Shiga Gaza Daga Masar

Rahotani daga Gaza na cewa ana sa ran kimanin motocin Agaji 200 su shiga yankin daga kasar Masar a yau Lahadi. Khaled Zayed, shugaban kungiyar

Rahotani daga Gaza na cewa ana sa ran kimanin motocin Agaji 200 su shiga yankin daga kasar Masar a yau Lahadi.

Khaled Zayed, shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar a arewacin Sinai, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, a yau ne ake sa ran manyan motocin agaji 200 za su shiga Gaza ta mashigar Karem Abu Salem (Kerem Shalom).

Karem Abu Salem na kan iyakokin Masar, Isra’ila da Gaza, kuma ta kasance mashiga ta biyu zuwa kudancin Gaza.

Mashigar Rafah da ke tsakanin Masar da Gaza, na rufe tun bayan da sojojin Isra’ila suka kwace iko da shi a ranar 6 ga watan Mayu.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Masar ta amince ta ba da damar shigar da kayan agajin da Majalisar Dinkin Duniya ke bayarwa zuwa Gaza na wani dan lokaci ta hanyar Karem Abu Salem har sai an samar da hanyoyin da doka ta shimfida na sake bude kan iyakar Rafah daga bangaren Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments