Hamas: Ba za mu amince da duk wata rundunar soji a cikin yankunanmu ba

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kakkausar suka ga duk wani yunkuri na girke sojojin kasashen ketare a cikin Falastinu. Kungiyar ta ce a

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kakkausar suka ga duk wani yunkuri na girke sojojin kasashen ketare a cikin Falastinu.

Kungiyar ta ce a cikin wani takaitaccen bayani da ta fitar, “Mu da dukkanin bangarorin gwagwarmayar Palastinawa muna tabbatar da hakkin al’ummarmu na samun dukkanin taimakon da suke bukata dangane da matsaloli na ayyukan jin kai da Isra’ila ta haifar a cikin yankunan zirin Gaza.”

Har ila yau kungiyar ta jaddada cewa, duk wata hanya ta kawo kayan agaji da suka hada da tashar ruwa, dole ne su zama a bude, ba tare da wani tarnaki ba.

Wani abin lura a nan shi ne, a safiyar jiya Juma’a, dimbin manyan motoci na hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, suka fara sauke kayayyakin jirgin ruwan agajin jin kai na farko da ya isa tashar ruwa da ke gabar tekun zirin Gaza.

Abin lura shi ne cewa manyan motocin na hukumar samar da abinci ta duniya sun samu rakiyar ma’aikatan hukumar a kan hanyarsu ta zuwa tashar jiragen ruwa.

Majiyoyin Falasdinawa na cikin gida sun ce manyan motocin za su yi jigilar kayan agajin zuwa yankunan kudancin zirin Gaza domin raba wa dubban daruruwan mutanen da suka rasa matsugunansu, musamman a yankin Al-Mawasi da ke yammacin Khan Yunis da Deir Al-Balah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments