An Raya Ranar Fada Da Masu Girman Kai Ta Duniya A Iran

A fadin kasar Iran, an gudanar da jerin gwano na turawa da ranar fada da masu girman kai ta duniya wacce ake yi a kowace

A fadin kasar Iran, an gudanar da jerin gwano na turawa da ranar fada da masu girman kai ta duniya wacce ake yi a kowace ranar 3 ga watan 8 na kalandar Iran ta hijira shamshiyya.

Wannan ranar ta samo asali ne daga ranar da daliban jami’oin Iran su ka  mamaye ofishin jakadanci Amurka dake Tehran a 1979 wanda aikinsa ya tashi daga na diplomasiyya zuwa leken asiri.

Bugu da kari, ofishin jakadancin na Amurka ya mayar da hankali wajen shirya makiric da makarkashiya ga jaririn juyin musulunci da bai fi watanni da kai wa ga samun nasara ba.

Wannan ranar ta zama ta nuna kin amincewa da halayyar girman kai da dagawa irin ta Amurka da sauran kasashe irinta, ta yadda a kowace shekara Iraniyawa a fadin kasa suke yin jerin gwano a cikin garuruwa da birane suna masu bayar da taken nuna kin jinin azzalumai.

Imam Khumain ya bayyana abinda daliban su ka yi da cewa shi ne juyin juya hali na biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments