Jaridar Ha’aratz ya bayyana wata sabuwar badakala da ta shafi fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila da ke da alaka da cin hanci da rashawa da kuma harin da aka kai gidansa
Jaridar ‘Ha’aretz’ ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cikakken bayani kan wata sabuwar badakala ta fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, da kuma kokarin gujewa gurfana a gaban kotu saboda harin da ‘yan gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon suka kai kan gidansa.
Jaridar ta ce: Netanyahu yana amfani da lamarin fashewar wani jirgi mara matuki ciki a gidansa a matsayin hujjar neman dage shari’ar da ake Shirin yi kansa a ranar 11 ga watan Disamba mai zuwa, inda ta ce: “Netanyahu yana amfani da uzurin cewa kungiyar Hizbullah za ta iya kai hari kan ginin kotun a birnin Qudus da jirgi maras matuki ciki a lokacin shari’arsa.”
Jaridar ta kara da cewa “Netanyahu na iya sake neman a dage shari’arsa, kuma da alama bai shirya fuskantar tuhumce-tuhumcen da ake masa ba domin kare kansa.”
Jaridar ta tabbatar da cewa: Akwai yunkurin kafa wata doka da za ta hana bayyana inda Netanyahu yake saboda dalilai na tsaro bayan da jirgin sama ya kai masa hari a gidansa kuma yana tsoron kada a kai hari a wurin taron nasa a majalisar dokokin Knesset da kuma kafa dokar hukunta duk wanda ya bayyana inda yake.