Tattaunawar tsagaita bude wuta da Amurka ta amince da ita na ci gaba ne a halin yanzu, mako guda gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Amurka, wanda kuma ya zo daidai da karuwar hasarar rayukan sojojin yahudawan sahayoniyya da kuma shan kashin da suke yi a fagen yaki a Lebanon, musamman gagarumar hasarar da suka yi a Black Oktoba, a cewar jaridun haramtacciyar kasar Isra’ila.
Yunkurin da Amurka da na yankin Gabas ta Tsakiya ke yi na ganin tattaunawar dakatar da bude wuta ya ci gaba sakamakon kin amincewar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da bukatarta na ci gaba da yaki da batun kin janye sojojinta daga Zirin Gaza, a halin yanzu bukatar neman bude wuta ta kunno kai a tsakanin jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar ta Isra’ila saboda bukatun kansu.
Bukatar dakatar da bude wutar ta zo ne karkashin jagorancin ministan tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila Yoav Galanat da babban hafsan hafsoshin soji Herzi Halevi, wadanda suka kara matsin lamba kan Fira ministan gwamnatin mamaya Benjamin Netanyahu don cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, a cewar jaridun yahudawan sahayoniyya.