Yawan Falasdinawa da suka yi shahada da jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya a Gaza sun kai 145,000
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar da rahoton kididdiga na yau da kullun kan adadin shahidai da wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da kai wa kan Zirin Gaza a rana ta 392 a jere.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a, ta bayyana cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun gudanar da kisan kiyashi sau 3 kan iyalan Falasdinawa a Zirin Gaza, da suka janyo shahidai 55 da kuma jikkata wasu 186 da aka kai su asibitoci.
Don haka an sanar da cewa: Adadin wadanda suka yi shahada a hare-haren sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya karu zuwa shahidai 43,259 da kuma jikkata 101,827 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.
Ma’aikatar lafiyar ta yi nuni da cewa: Har yanzu akwai adadin wadanda hare-haren suka ritsa da su a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, kuma motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farar hula ba za su iya isa gare su ba.