Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Fifita Shirin Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Babban fifikonta shi ne samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya Kakakin ma’aikatar

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Babban fifikonta shi ne samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Bagha’ei ya jaddada cewa: Babban fifikon Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya shi ne samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, bisa la’akari da cewa kawo karshen munanan ayyukan yahudawan sahayoniyya aiki ne na jin kai, da’a da kuma shari’a kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

Baqa’i ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na mako-mako da yake gudanarwa, inda ya bayyana cewa: A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, hukumomin diflomasiyya sun yi kokarin hana ‘yan ta’addar yahudawan sahayoniyya aiwatar da kashe-kashen gilla da kara tada wutan yaki a Gaza da Lebanon da kuma yada shi zuwa sauran yankin, yana mai cewa wannan tuntubar juna ta fara ne da yunkurin ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iran ya kai zuwa kasar Lebanon.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kara da cewa: Baya ga shawarwarin diflomasiyya da tafiye-tafiye zuwa kasashen yankin, ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya kuma yi ta wayar tarho da jami’ai daban-daban tare da yin shawarwari mai kyau kan hana yaduwar rikici. Sakon ministan harkokin wajen kasar Iran a wadannan tafiye-tafiye ya fito fili karara, musamman game da inganta da fadada alaka da kasashen makwabta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments